Isa ga babban shafi

An tsamo gawarwakin bakin haure 901 a gabar ruwan Tunisia cikin watanni 6

Jami'an tsaron gabar ruwan Tunisia sun ce sun tsamo jimillar gawarwakin bakin haure 901 da suka nutse a teku kasar yayin kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai daga kasar.

Jerin kananan jiregen ruwan da jami'an tsaron Tunisia suka kwace, bayan da bakin haure suka yi amfani da su wajen kokarin tsallaka teku don shiga Turai.
Jerin kananan jiregen ruwan da jami'an tsaron Tunisia suka kwace, bayan da bakin haure suka yi amfani da su wajen kokarin tsallaka teku don shiga Turai. REUTERS - JIHED ABIDELLAOUI
Talla

Ministan harkokin cikin gidan Tunisia Kmael Feki, ya ce an ciro gawarwakin masu yawan gaske ne a tsakanin ranar 1 ga watan Janairu zuwa 20 ga watan Yulin wannan shekara, lamarin da ke bayyana adadi irinsa na farko da aka gani na bakin hauren da suka rasa rayukansu yayin kokarin isa Turai.

Feki ya shaidawa majalisar kasar cewa daga cikin gawarwakin mutane 901 da aka gano akwai 'yan Tunisia 36 da kuma bakin haure 267, yayin da sauran ba a gano ko su wanene ba.

Kasar Tunisia da ke arewacin Afirka na fuskantar matsalar kwararar bakin haure a shekarar bana, wadanda ke hankoron tashi daga gabar ruwan kasar don tsallaka teku don shiga kasashen Turai, lamarin ya janyo yawaitar nutsewar kwale-kwalen ‘yan ci ranin tun kafin ma su yin isa, wadanda akasarinsu suka fito daga kasashen kudu da Saharar Afirka.

Tuni dai Tunisia ta maye gurbin Libya a matsayin babbar cibiyar da ‘yan ci rani daga Afirka ke bi a kokarinsu na ficewa daga nahiyar, don gujewa matsalolin da suka hada da talauci, da tashe tashen hankula, cike da fatan samun kyakkyawar rayuwa a Turai.

Mafi yawan kwale-kwalen da ke dauke da bakin haure na tashi ne daga gabar tekun da ke birnin Sfaxn a kudancin Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.