Isa ga babban shafi

Mahukuntan Gambia sun sanar da ceto bakin haure kusan 300 cikin mako biyu

Mahukuntan kasar Gambia sun sanar da ceto bakin haure da ke yukurin tsallakawa zuwa turai, kuma suka makale a Saharar Libya kusan 300 cikin mako 2.

Une embarcation utilisée par des migrants en provenance du Maroc sur une place de l'île de Gran Canaria en 2016 (image d'illustration).
Une embarcation utilisée par des migrants en provenance du Maroc sur une place de l'île de Gran Canaria en 2016 (image d'illustration). AP - Javier Bauluz
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Gambia ce ta sanar da hakan, tana mai cewa cikin mutane 296 da ta ceto din, guda 140, yan asalin kasar  an ceto su a tsakanin ranakun 21 ga watan Yunin jiya zuwa 4 ga watan da muke ciki na Yuli.

Wadannan sabbin alkalma na zuwa ne bayan wanda mahukuntan kasashen Senegal da Morocco da Mourtania suka fitar, inda suma suka ce sun ceto bakin haure kusan dubu 1 a saharar ta Libya suna yunkurin tsallakawa zuwa turai, kuma cikin su 231 yan asalin Gambia ne.

Nahiyar Africa na fuskantar matsalolin bakin haure a ciki da wajen ta, don kuwa ko a ranar Alhamis din da ta gabata sai da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bukaci Tunisia ta yi gaggawar dawowa cikin hayyacin ta bayan da ta fatattaki bakin haure bakar fata fiye da 3000 zuwa iyakar ta da Libya.

Daukar Matakin ya biyo bayan tarzomar kin jinin baki da ta tashi karo na biyu a kasar bayan kisan wani dan asalin kasar da baki suka yi, abinda ke zuwa bayan matsin lamba da bakin ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.