Isa ga babban shafi

An fara babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 78 a New York

Daga wannan Talata, 19 zuwa 23 ga watan Satumba, sama da jagororin kasashen duniya 100, da dubban jami’an diflomasiyya ne za su hadu a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York na Amurka don samar da masalaha a game da yadda za su tinkari kalubalen da duniya ke fuskanta.

Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya,l Antonio Guterres.
Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya,l Antonio Guterres. AP - Richard Drew
Talla

Taron, wanda shine karo na 78, zai mayar da hankali ne a kan sake gina yarda, tare da farfado da hadin kan duniya, domin gaggauta cimma muradan karni, wajen zaman lafiya da kuma ci gaban al’umma.

Wannan taron na zuwa ne a daidai lokacin duniya ke samun koma baya irin wadda ba a taba gani ba ta bangaren ci gaba, inda talauci da karancin abinci ke ta’azzara, ga kuma yaki da hauhawar farashin kayayyaki.

Shugaban wannan taro na 78 shine wakilin kasar Trinidad da Tobago na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Dennis Frances, wanda aka zaba a watan Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.