Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin barkewar cututtuka a Libya
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa birnin Derna, wanda ya fuskanci matsalar ambaliya, inda dubban mutane suka mutu mako guda da ya wuce yana fuskantar barazanar barkewar cututtuka da za ta iya haifar da wata matsala mai tayar da hankali.
Wallafawa ranar:
Mummunar ambaliyar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 3, da bacewar dubbai ta zo ne a lokacin a kasar, wanda ke arewacin nahiyar Afirka ta fuskanci mummunar barna daga mahaukaciyar guguwar Daniel.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce al’ummar yankin sama da dubu 30 ne ke matukar bukatar tsaftataccen ruwan sha da sauran mahimman kayayyaki, a yayin da suke dada nutsewa cikin hadarin kamuwa da cutuka da suka hada da kwalara, amai da gudawa, karancin abinci mai gina jiki da sauran su.
Kwamitin da Majalisar Dinkin Duniya ta aike Libya don taimaka wa wadanda mahaukaciyar guguwar Daniel da kuma ambaliya suka yi wa ta’adi su na ta aikin bada agaji ba kakkautawa.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da suka hada da Asusun tallafa wa Yara na UNICEF, Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Hukumar Samar da Abinci sun kasance a cikin birnin Derna su na taimaka wa wadanda suka tsira daga iftila’in da ya afka wa birnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu