Isa ga babban shafi

Bangarorin da ke rikici da juna za su hada hannu don tunkarar ibtila'in Libya

Bangarorin da ke rikici da juna a Libya sun amince da hada hannu wajen taimakon dubunnan mutanen da mummunar ambaliyar ruwan kasar ta shafa a gabashin birnin Derna mai tashar jiragen ruwa.

Akalla mutane dubu 6 suka mutu a ibtila'in ambaliyar ta Libya.
Akalla mutane dubu 6 suka mutu a ibtila'in ambaliyar ta Libya. AFP - -
Talla

Wannan dai na matsayin karon farko da bangarorin biyu suka amince da aiki tare kan manufa guda tun bayan farrakarsu biyo bayan juyin juya halin kasar ta Libya a shekarar 2011.

A daren Litinin din da ta gabata ne ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da kauyuka da dama a birnin na Derna da ke gab da teku, biyo bayan kakkarfan ruwan saman da ake shafe daren Lahadi ana yi wanda masana suka ce shi ne mafi yawa da Libya ta taba fuskanta a tarihi.

Zuwa yanzu fiye da mutane dubu 10 ne suka bace tun bayan faruwar ibtila’in wanda ya kashe fiye da mutane dubu 6 yayinda kungiyar agaji ta Red Cresent ke cewa akwai tsammanin adadin wadanda suka bace su iya karuwa saboda har yanzu hankula basu nutsa ba, barre iyalai suka kai ga gane ‘yan uwansu da suka bace.

Tuni dai agajin kasashe ya fara isa kasar ta Libya a bangare guda kuma bangarorin na gwamnati Khalifa Haftar da ke jagorancin gabashin kasar da kuma gwamnati mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya suka hada hannu don taimakon tarin wadanda ambaliyar ruwan mafi muni a tarihi ta afkawa a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.