Sakacin mahukunta ne ya haifar da ballewar madatsun ruwan Derna a Libya
Rahotannin tsawon shekarun da dama sun nusar da gwamnatocin kasar Libiya irin mummunan yanayin da madatsun ruwan Derna guda biyu ke cikiAl’amarin da sannu a hankali ya kai ga haddasa mummunan bala’in ya faru a ranar lahadin 8-9 ga watan satumabar 2023 da muke ciki, bayan sake fadakar da mahukumtan, kwanaki 6 kafin isar guguwar Daniel, da ta haifar da ambaliyar ruwa a garin Derna, inda sama da mutane dubu 11 suka rasa rayukansu a ya yinda wasu sama da dubu 10 suka bata.
Wallafawa ranar:
Madatsun ruwan da aka gina a yankin yammacin Derna, kamar sauran madatsan ruwan kasar ta Libiya, sun nuna alamar tsatsagewa tun cikin 1998 .
Duk da haka kuma, mahukumtan na Libiya sun ci gaba da kawar da kai, kan gine ginen tun lokacin mulkin Mouammar Kadhafi daga shekarar 1969 zuwa 2011 da kuma wadanda suka maye urbinsu daga 2011 zuwa yau 2023.
A ranar lahadin da ta gabata sakamakon karfin ruwan da suka sauka a Derna, madatsar ruwan ta farko, cewa da madatsar ruwan Abou Mansour, mai dauke da kimanin lita miliyan 22.5 da ke tazarar kilo mita 13 da Darna ta balle, inda ta saki tanatanan taguwowin ruwan da suka fada ga madatsar ta biyu, cewa da madatsar Al-Bilad, mai dauke da kimanin lita miliyan 1,5, da kuma ke da nisan kilo mita daya kacal da garin na Derna dake yankin gabar Tekun Libiya.
Kasancewar madatsar a kusa da garin na Derna ne, ya sa mawuyacin abu ne ruwan ya iya kwararewa fadawa garin da karfi a dai dai lokacin da mazaunasa ke tsakiyar sharar barci da tsakkiyar dare, da ya sa Darna ya kasance babbar hanyar da ruwan suka shatawa kansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu