Isa ga babban shafi

Har yanzu akwai fatan iya ceto masu rai a ambaliyar ruwan Libya- Red Cross

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce har yanzu akwai yiwuwar samun sauran masu rai a yankunan da laka rufe bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta faru a Libya, dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke kaddamar da wani asusun dala miliyan 71 don taimakon kasar ta arewacin Afrika.

Jami'an agajin da ke ci gaba da aikin ceto a Libya.
Jami'an agajin da ke ci gaba da aikin ceto a Libya. AP
Talla

Jami’an kungiyar agajin na ci gaba da aikin laluben cikin laka da baraguzen gine-ginen da ambaliyar ruwan ta rusa a yankin da Ibtila’in ya faru da nufin lalubo kusan mutum dubu 10 da suka bace tun bayan faruwar lamarin a ranar Litinin.

Sanarwar ta Red Cross tare da Red Crescent suka fitar yau juma’a, ta ruwaito Tamer Ramadan babban jami’in kungiyar na cewa jami’ansu baza su fitar da rai kan yiwuwar ceto wadanda suka bace a ibtila’in ba, lura da yadda ko a yau aka yi nasarar ceto wasu da ransu.

Akwai dai Iyalai da dama da wannan ibtila’in da ya faru cikin dare yayi awon gaba da su gabaki daya, lamarin da ya kai ga kisan akalla mutum dubu 6 kamar yadda gwamnatin kasar ta bayar da alkaluma.

Ana ci gaba da gano gawarwakin mutanen da suka mutu a ibtila'in ambaliyar ruwan na Libya mafi muni a tarihin kasar.
Ana ci gaba da gano gawarwakin mutanen da suka mutu a ibtila'in ambaliyar ruwan na Libya mafi muni a tarihin kasar. REUTERS - ESAM OMRAN AL-FETORI

Majalisar Dinkin Duniya ta ce har zuwa yanzu ba a kai ga gano girman matsalar ba, lura da cewa sai a yanzu ne aka samu amincewar bangarori biyu da ke gaba da juna a kasar don aiki tare wajen tunkarar matsalar mafi muni a tarinin Libya.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da neman tallafin dala miliyan 71 don agazawa akalla mutane dubu 250 da ke tsananin bukatar agajin gaggawa kari kan wasu dubu 884 da suma ke bukatar dauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.