Isa ga babban shafi

Muna gaf da cimma muradun samar da ci gaba a duniya - MDD

A ranar Talata 19 ga watan Satumban nan na shekarar 2023, a birnin New York na kasar Amruka, majalisar dinkin duniya za ta buda zaman taronta, kan manufofin samar da ci gaba mai dorewa a duniya (ODD), nan da shekara 2030.

Amina Mohammed
Amina Mohammed AP - Bebeto Matthews
Talla

Mataimakiyar shugaban Majalisar Dinkin Duniya,  Amina Mohammed, ta bayyana cewa, zamanin wadannan manufofi bai wuce ba, illa dai kawai a na bukatar  rungumar wata sabuwar turbar siyasa ne.

Ta ce a wajensu, manufofin samar da ci gaban mai dorewa guda 17 na ODD ya kamata a gudanar da su ne tare da al’umma, ta hanyar zuba jari a cikin tattalin ariziki, haka kuma a cikin mutunta mahalli.

Sai dai kuma, me hakan ke nufi ? idan kuka lura da manofofin farko guda 6, sun shafi bangaren zuba jari ne, da ake bukata wajen kyautata rayuwar al’umma, wadanda su ka hada da fannin kiyon lafiya, samar da cimaka, abinci mai gina jiki , ruwa da kuma tsafta , yanci jinsi, da yancin mata da kankanan yan mata.

Dukkanin wadannan batutuwa ana iya aiwatar da su ne karkashin manufofi guda bakwai, da suka shafi tattalin ariziki, da kuma ta yadda  za mu  zuba jarin domin ganin an bunkasa tattalin arzikin.

A game da banbancin da ake samu kuma, idan za a zuba jari a fanin makaranta, ba za a yi shi saboda ‘yan maza ba kawai, za a yi shi saboda su ma ‘yan mata. Idan har za ku zuba jari a fanin ilimi, to doli ne ku tabbatar da cewa, tsarin ya yi la’akari da zurfin basira da kuma raunin da ‘yan mata ke da shi.

Haka kuma ya na da matukar muhimmanci ga kasashen duniya su gane cewa, wadannan manufofi na duniya ne. Haka kuma Manufarmu ita ce, ganin an yi amfani da kudaden  bisa adalci, ba tare da an yi amfani da su a bangare daya na duniya ba kawai.

Wannan zai baiwa kasashe matalauta  damar  samun kudade ba sai sun yi roko ko bara ba, wajen ganin  su ma sun  samu damar kai wa ga kudaden tafiyar da ayukan ci gaban dai dai da kowace kasa ta duniya.

Yancin da zai ba su damar amfana da kudin ruwa na bai daya, wajen gina makarantu, samar da masana’antu. Bugu da kari manufofin karshe, sun ta’alaka ne kan hakikanin matsalar dumamar yanayi, shugabanci na gari, kyautata hukmomi, da kuma aiki da  dokoki, tare da yin aikin hadin guiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.