Isa ga babban shafi
SAUYIN YANAYI

Sauyin yanayi: Dubban masu zanga-zanga sun yi tattaki a birnin New York

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga  kan titinan birnin New York na kasar Amruka, inda su ka bukaci kara kaimi wajen yaki da matsalar dumamar yanayi a duniya, yayin da ake jajibirin  buda gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya (AGNU).

wata zanga zangar nuna rashin amincewa da dumamar yanayi  à Los Angeles, a Californie, juma'a 15 satumba.
wata zanga zangar nuna rashin amincewa da dumamar yanayi à Los Angeles, a Californie, juma'a 15 satumba. AFP - FREDERIC J. BROWN
Talla

Masu zanga zangar da suka fito daga kungiyoyi da gungunan fararen hula  sama da 700, na dauke da alluna da kwalaye ne, dake dauke da rubutu  da ke kira ga shugaban Amruka Joh Biden da ya kawo karshen amfani da tsohon  makamashi mai gurbata yanayin duniya, ‘‘tsohon makamashin na kashe mu, ban yi zabe domin gobara ko ambaliyar ruwa ba’’.

Shugaban Amruka, Joh Bide, na daga cikin jerin shuwagabanin kasashen duniya da a yau litanin, za su halarci zauren Majalisar dinkin duniya, da zai buda babban zaman taronsa  a gobe talata.

Analilia Mejia, daraktar kungiyar farar hula ta  Center for Popular Democracy (cibiyar bunkasa demkradiyar al’umma) ta ce, su na tattakin ne, domin neman mahukumta su dau matakan da suka dace, wajen takawa matsalar dake haifar da dumamar yanayin birki.

A cikin wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan dumamar yanayin da aka fitar a cikin wannan wata, masana sauyin yanayi na duniya, sun bayyana  cewa, ana iya rage fitar da turiri mai guba dake haifar da dumamar yanayi duniya nan da 2025,  idan har da gaske mahukumtan duniya  su ke, su na son su cimma muradun rage dumamar yanayin na duniya, kamar yadda manufofin yarjejeniyar birnin Paris ta tanada.

 Yarjejeniyar Paris, da aka rattabawa hannu a 2015, ta zaburar da samar da hanyoyi da dama da za su kyautata yanayin na duniya. Sai dai kuma, har yanzu akwai jan aiki ta ko wane fanni, kamar yadda rahoton zaman taron dumamar yanayi na COP28 da za a gudanar  a birnin Dubai na kasar Daular Laraba  a karshen wannan shekara ta 2023 ya nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.