MDD ta yi gargadi kan karuwar wariyar da mata ke fuskanta a dukkan matakai
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yadda mata ke ci gaba da fuskantar wariya baya ga rashin samun cikakkun damarmaki a bangarorin da suka shafi tattalin arziki da siyasa, duk da fafutukar tabbatar da daidaiton jinsi da kungiyoyi ke ci gaba da yi.
Wallafawa ranar:
Rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar a yau alhamis ya ruwaito, Sarah Hendriks shugabar sashen tabbatar da hakkokin mata a majalisar na cewa an gaza ta kowacce fuska wajen bai wa matan damarmakin da su ke bukata ko kuma sanya su a guraben da suka cancanta.
Rahoton ya ce kama daga yaki da talauci ko kuma samun damar ilimi koma wakiltar al’umma a mukaman siyasa dama jagorantar lamurran tattalin arziki na kasashe, matan basa samun damarmaki sabanin takwarorinsu maza.
Rahoton ya ce alkaluman da aka tattara na nuna cewa ko kusa ba a kama hanyar cimma muradan karni 17 da Majalisar ta gabatar a shekarar 2015 kuma ta ke fatan cimmasu nan da shekarar 2030 ba.
A cewar rahoton halin da rayuwar mata ke ciki a kasashe ya yi hannun riga da muradan majalisar da ke fatan samar da daidaito tsakaninsu da takwarorinsu Maza, batun da ke nuna akwai tafiya mai nisa gabanin samun nasara a fafutukar.
Wasu daga cikin muradan da Majalisar ke fatan cimmawa nan da shekarar 2030 akwai kawo karshen wariya da kuma daina yi wa matan kaciya sai samar da daidaito a matakan aiki da basu damar shiga harkokin siyasa sai kuma samun cikakkiyar kulawar lafiya.
Sai dai Majalisar ta ce kusan dukkanin muradan sun hadu da cikas ta yadda a duk shekara mata miliyan 245 da shekarunsu ya haura 15 ke fuskantar musgunawa daga abokanan zamansu yayinda duk mace 1 cikin 5 ke fuskantar aure gabanin kai wa shekaru 18.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu