Isa ga babban shafi

Kotun Kolin Faransa ta goyi bayan hana dalibai mata sanya abaya

Kotun Kolin Faransa ta amince da sabuwar dokar gwamnatin kasar game da haramta wa mata Musulmai amfani da hijabi ko kuma rigar abaya don rufe jikinsu a cikin manyan makarantu. 

Wasu mata Musulmai sanye da suturar da ta rufe jikinsu.
Wasu mata Musulmai sanye da suturar da ta rufe jikinsu. © @Reuters
Talla

Kungiyoyin Musulmi na Action for the Rights of Muslim da Council of the Muslim Faith  suka shigar da kara don kalubalantar dokar hana matan sanya hijabin, amma a yayin yanke hukuncin, kotun ta ce ba za ta iya amince wa da bukatarsu ba kasancewar rufe jikin da mata ke yi ya saba wa dokokin da suka haramta nuna wata alamar addini a guraren neman ilimi. 

Baya ga haka, kotun ta yi karin haske kan cewa, koda filayen wasanni ma, bai kamata mata su rika rufe jikinsu ba kasancewar hakan na jefa fargaba a zukatan ‘yan wasa da kuma rashin sakin jiki.  

Da ma tun ba yanzu ba Hukumar Kula da Kwallon Kafar Kasar ta haramta wa mata Musulami amfani da duk wani nau’i na suturar da za ta rufe jikinsu, a cewarta, filayen wasanni ba wajen tallata addini, siyasa ko al’ada ba ne, waje ne na nuna ‘yan uwantaka da son juna. 

Wasu dalibai a wata makaranta
Wasu dalibai a wata makaranta AFP - LOIC VENANCE

Sai dai tun wancan lokaci, kungiyar mata Musulumi ‘yan kwallon kafa ta shigar da kara kuma har kawo yanzu kotu ba ta yanke hukunci ba. 

 

Tuni dai wannan al’amari ya tayar da zazzafar muhawar tsakanin manyan ‘yan siyasa a kasar, yayin da wata wallafa da Marine Lepen mai ra’ayin rikau ta taba yi a baya da ke cewa “Dole ne mu hana hijabi a filayen wasa, za mu zartas da wannan doka kuma sai mun tabbatar ana biyayya gare ta" ta fara yawo a tsakanin jama’a a kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.