Isa ga babban shafi

Rasha ta gindaya sharudda kan yiwuwar komawa yarjejeniyar fitar da hatsi

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce kasar za ta koma cikin yarjejeniyar fitar da hatsin da ta fice a baya-bayan nan idan har aka iya cika sharuddan da ta gindaya wadanda ke kunshe da bukatun ta, bayan da shugaban ya yi ikirarin cewa yarjejeniyar ta rasa dukkanin manufofin da tun farko aka kulla ta domin su.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. © Alexander Kazakov / AP
Talla

Wannan ne karon farko da shugaban na Rasha ke yin tsokaci tun bayan ficewar kasar daga yarjejeniyar a makon jiya bayan da ta kawo karshe, lamarin da ya tayar da farashin hatsin a kasuwannin duniya sakamakon gaza iya fito da shi ta tekun Black Sea duk da yadda kaso mai yawa na kasashe suka dogara da Rasha da Ukraine wajen samun alkama.

A kalamansa yayin jawabinsa a gaban taron kusoshin gwamnatinsa Putin ya bayyana cewa Rasha ba za ta iya ci gaba da yarjejeniyar a halin da ta ke yanzu ba, saboda rashin amfaninta.

Putin ya bayyana cewa ko shakka babu Rasha za ta koma iya komawa cikin yarjejeniyar amma bisa sharadi guda wato bayan an kammala an aminta da dukkanin bukatun da ta mika tun farko gabanin amincewa da shiga yarjejeniyar.

Cikin wadannan bukatu kuwa a cewa Putin har da janye dukkanin takunkuman da aka kakaba kan hatsi da kuma takin da kasar ke fitarwa ketare.

Tsawon watanni Kenan Rasha na korafi yadda bangarrorin da ke cikin wannan yarjejeniya suka gaza mutunta bukatar da ta shigar na ba ta damar fitar da kayakinta kasuwannin Duniya salin alin.

A cewar Putin kasashen yammaci na amfani da yarjejeniyar wajen biyan bukatunsu maimakon taimakawa kasashen da ke da bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.