Isa ga babban shafi

Hare-hare sun kashe fararen hular Ukraine dubu 9 cikin kwanaki 500 da fara yakin Rasha

Yau ake cika kwanaki 500 da faro mamayar Rasha a Ukraine bayan kaddamar da yakinta a ranar 24 ga watan Fabarairun 2022, yakin da zuwa yanzu ya lakume rayukan fararen hula fiye da dubu 9 ciki har da kananan yara 500.

Wasu Sojin Ukraine a yankin da Rasha ta farmaka.
Wasu Sojin Ukraine a yankin da Rasha ta farmaka. AP - Evgeniy Maloletka
Talla

Wata sanarwa da hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai sanya idanu kan yakin na Rasha a Ukraine ta fitar a jiya Juma’a ta yi gargadin cewa alkaluman rayukan fararen hulan da suka  salwanta a yakin ko shakka babu za su iya karuwa lura yadda aka gaza tattara wasu alkaluman mace-mace a hukumance.

Shugaban hukumar ta HRMMU Noel Calhoun ya bayyana cewa rayukan fararen hula na ci gaba da salwanta a yakin musamman fararen hular da basu ji ba basu gani ba.

Hari na baya-bayan nan da Rasha ta kaddamar shi ne na ranar 27 ga watan Yunin da ya gabata wanda ya kashe fararen hula 13 ciki har da kananan yara 4 a yankin Kramatorsk na gabashin Ukraine.

Yadda hare-haren Rasha ke ci gaba da salwantar da rayukan fararen hula a Ukraine.
Yadda hare-haren Rasha ke ci gaba da salwantar da rayukan fararen hula a Ukraine. AP - Mykola Tys

A cewar jami’in duk da cewa an samu raguwar rasa rayukan fararen hula idan aka kwatanta da dimbin adadin da suka mutu a farko faro mamayar amma tsakanin watan Mayu da Yunin da ya gabata an sake ganin hauhawar rasa rayukan fararen hula.

Ko a alhamis din da ta gabata, sai dai wasu hare-hare suka kashe wasu mutane 10 tare da jikkata wasu 37 a yammacin birnin Lviv tazara mai nisa da yankin da yakin ke faruwa.

Kungiyoyin kare hakkin dana dam da Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da kiraye-kirayen ganin hare-haren sun daina shafar fararen hula.

Tuni dai kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta bude shafin bincike ta hanyar amfani da hujjojin da Ukraine ta gabatar mata game da zargin shugaba Vladimir Putin da aikata laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.