Isa ga babban shafi

Kasashen Afrika za su yi fama da tsadar abinci - MDD

Masu aikin agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa, za a samu sabuwar tsadar farashin kayayyakin abinci wadda za ta shafi miliyoyin mutanen da ke fama da yunwa a kasashen kuryar gabashin Afrika muddin aka kawo karshen yarjejeniyar fitar da hatsi daga yankin Tekun Black Sea.

Akasarin kasashen kuryar gabashin Afrika sun dogara ne da hatsin da ake nonawa a Ukraine.
Akasarin kasashen kuryar gabashin Afrika sun dogara ne da hatsin da ake nonawa a Ukraine. REUTERS - KACPER PEMPEL
Talla

Gwamnatin Rasha ta sha yin barazanar janyewa daga wannan yarjejeniya ta fitar da hatsin daga yankin Tekun Black Sea wadda Majalisar Dinkin Duniya da Turkiya suka  jagoranci rattaba hannu a kanta a cikin watan Yulin bara.

An dai cimma yarjejeniyar ce tsakanin Rasha da Ukraine da ke yaki da juna, yayin da Moscow ke cewa, muddin aka ki janye takunkuman da ke kanta na hana ta safarar hatsinta da takinta ta jiragen ruwa, to lallai ita ma za ta fice daga yarjejeniyar.

Wani jakadan Ukraine ya ce, yana da yakini kusan 100 bisa 100 kan cewa, Rasha za ta ki rattaba hannu idan lokacin sabunta yarjejeniyar ya kai.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na ganin cewa, wargajewar wannan yarjejeniya za ta fi yin mummunan tasiri kan kasashen da ke kuryar gabashin Afrika da akasarinsu suka dogara da hatsin da ake noman su a Ukraine.

Masu aikin agaji na Majalisar Dinki Duniyar sun ce, kimanin mutanen yankin miliyan 60 na ci gaba da fuskantar barazanar karancin abinci a yanzu haka, abin da ya sa ake fargabar  cewa, halin da suke ciki zai tsananta idan yarjejeniyar hatsin ta kawo karshen bagatatan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.