Colombia: An gano wasu yara 4 a raye bayan hadarin jirgin sama
Shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ya sanar da cewa an gano wasu ‘yan asalin kasar yara hudu da suka bace sama da wata guda a dajin Amazon na Colombia bayan wani karamin jirgin saman da suke ciki ya yi hadari.
Wallafawa ranar:
Da yake shaidawa manema labarai shugaban kasar Gustavo Petro yace an ga abin mamaki ranar Jumma’a, lokacin da jami'an saro sama da 200 da aka baza a dajin na Amazon suka gano yaran, sama da kwanaki 40 bayan da bacewarsu.
Yace yaran na cikin alamun tagayyara, amma suna samun kulawar likitoci.
Yaran 'yan gida daya - masu kimanin shekara 13 da 9 da kuma hudu da kuma daya, sun ja hankali sosai a yunkurin ceto su da gwamman sojoji ke yi a dajin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu