Isa ga babban shafi

Sojojin Colombia sun murkushe masu safarar miyagun kwayoyi a yankin Gulf

Akalla mutane tara ne aka kashe jiya talata a arewa maso yammacin Colombia a wani samame da sojoji suka kai kan kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi a yankin Gulf, wanda aka kama Shugaban su a watan Oktoban da ya gabata.

Ministan tsaron Colombia  Diego Molano  tar da rakiyar dakarun kasar yayin samame kan yan kungiyar Otoniel
Ministan tsaron Colombia Diego Molano tar da rakiyar dakarun kasar yayin samame kan yan kungiyar Otoniel Handout Ministerio colombiano de Defensa/AFP
Talla

An fara aikin ne da sanyin safiyar Talata kuma ana ci gaba da gudanar da wannan aiki har jiya da maraice lokacin da ministan tsaron kasar, Diego Molano ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu an gano mutuwar mutane tara a farmakin da ake kai wa 'yan kungiyar ta masu miyagun kwayoyi.

A cikin watan Oktoban shekarar 2021 ne aka kama Shugaban wannan kungiya, Bayanan hukumomin tsaro sun ce an kama Otoniel da asalin sunansa shi ne Dairo Antonio Usuga, a kusa da daya daga cikin manyan ofisoshinsa a yankin Necocli, dake kusa da kan iyaka da Panama.

Shugaban kungiyar dake safarar miyagun kwayoyi a yankin Gulf na kasar Colombia
Shugaban kungiyar dake safarar miyagun kwayoyi a yankin Gulf na kasar Colombia Handout Colombian army/AFP/Archivos

Sojoji akalla 500 tare da jirage masu saukar ungulu 22 gami da taimakon hukumomin tsaron Ingila da Amurka ne suka kai samamen da ya basu nasarar cafke Otoniel a yankin Necocli, inda a kokarin hakan dan sanda 1. ya rasa ransa.

Hodar ibilis da dakarun kasar colombia suka kama yayin samame da suka kai yankin Gulf
Hodar ibilis da dakarun kasar colombia suka kama yayin samame da suka kai yankin Gulf AFP/Archivos

Hotunan da gwamnati ta fitar sun nuna Otoniel mai shekaru 50 cikin ankwa yayin da kuma sojoji ke kewaye shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.