Panama da Colombia sun fitar da sabon tsari da ya shafi 'yan cin rani
Kasashen Panama da Colombia sun cimma yarjejeniya bai daya na ganin sun baiwa ‘yan cin rani dake neman shiga Amurka damar bi ta kasashen ba tareda wata tsongoma ba.
Wallafawa ranar:
Kasashen sun bayyana cewa tsarin zai shafi yan cin rani da ya dace sun amfana da wadanan matakai, kasashen biyu za su ci gaba da aiki kafada da kafada don gujewa yan cin rani fadawa cikin yanayi marar kyau da za ta kai su ga halaka wajen tsallakawa ta ruwa da makamancin haka.
Tsawon makonni kenan da tarin yan cin rani daga kasashen Haiti musaman yara kanana da mata masu ciki ke zaman jira a tashar jiragen ruwan Colombia, suna dakon jiragen da za su ficewa da su kan iyaka da Panama.
Wasu alkaluma na dada nuni cewa a shekara ta 2020 an samu raguwar yan cin rani sabili da cutar covid 19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu