Tunisia - 'Yan Ci Rani
'Yan ci rani 43 sun nutse a gabar ruwan Tunisia
Jami’an agaji a Tunisia sun sanar da bacewar akalla mutane 43 sakamakon kifewar wani jirgin ruwa dauke ‘yan ci rani 127 a gabar ruwan kasar dake yankin kudu maso gabashi.
Wallafawa ranar:
Talla
Kungiyar agajin gaggawa ta Red Crescent dake kasar ta Tunisia ta ce an samu nasarar ceto 84 daga cikin ‘yan ci ranin da suka nutse, yayin da har yanzu ake laluben ragowar 43.
Bayanai sun ce ‘yan ci ranin dake neman. tsalaka teku zuwa nahiyar Turai sun fito ne daga kasashen Chadi, Eritrea, Sudan, Masar da kuma Bangladesh.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu