Isa ga babban shafi

Kungiyar FARC ta Colombia ta shirya shiga tattaunawar zaman lafiya da gwamnati

Kungiyar ‘yan tawayen da ke dauke da makamai ta rusasshen kungiyar FARC ta Colombia ta ce a shirye take ta fara tattaunawar zaman lafiya da gwamnati daga ranar 16 ga watan Mayu.

Tattaunawa tsakanin gwamnati da yan kungiyar FARC a Colombia
Tattaunawa tsakanin gwamnati da yan kungiyar FARC a Colombia © YezidCampos
Talla

A wata sanarwa da ta fitar,kungiyar ta sanar da duniya cewa wakilanta sun shirya shiga tattauna da gwamnatin Colombia,a ranar 16 ga watan Mayu na wannan shekara.

Da take magana a taron shugabannin EMC, mai magana da yawun kungiyar Angela Izquierdo ta kara da cewa: suna fatan za a iya cimma nasarar da matsaya da nufin cimma zaman lafiya mai dorewa  a hukumance.

Manyan shugabannin EMC sun yi taro a wata gona a yankin kudancin San Vicente del Caguan tun daga farkon watan Afrilu, gami da tuntubar juna da al'ummomin yankunan da ke karkashin ikon EMC, don tsara dabarun tattaunawar zaman lafiya.

Manyan Shugabanin sun hada da Ivan Mordisco, wanda gwamnati ta yi ikirarin kashe shi a bara.

Tsofin yan Tawayen FARC na kasar Colombia
Tsofin yan Tawayen FARC na kasar Colombia © Marcela Manrique

Wasu ‘yan adawar sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2016 da ta kai ga rugujewar kungiyar ‘yan tawaye mafi girma da ban tsoro a yankin Latin Amurka, wato ‘yan tawayen FARC, yayin da wasu kuma daga baya suka koma cikin rukunin bayan sun kasa komawa rayuwa kamar farar hula.

Shugaban kasar Colombia Gustavo Petro mai barin gado na farko a kan karagar mulki tun watan Agustan da ya gabata, ya ci gaba da tattaunawa da 'yan tawayen FARC da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai da ke ci gaba da yakin basasa  da kuma yakar masu fataucin miyagun kwayoyi da albarkatun ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Yan kasar Colombia masu ra'ayuin zaman lafiya
Yan kasar Colombia masu ra'ayuin zaman lafiya VW Pics/Universal Images Group v - VW Pics

Shugaban kasar Petro ya hau kan karagar mulki ne da shirin samar da "zaman lafiya baki daya" a kasar da ta yi fama da tashe-tashen hankula na shekaru da dama.

A shirin shugaban kasar na samar da zaman lafiya, akwai batun tsagaita bude wuta na tsawon watanni shida tare da ‘yan tawayen FARC da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai tun ranar 1 ga watan Janairu.

A makon da ya gabata, gwamnati ta ce ana "karfafa shirin zaman lafiya da EMC."

An kiyasta yawan ya’an kungiyar ta EMC kimanin mayaka dubu 3,000 da ke aiki musamman a cikin Amazon, a gabar tekun Pacific da kuma kusa da kan iyaka da Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.