Ana zargin tsohuwar kungiyar FARC da dibar yara 18,000 cikin aikin soji
Wata kotu ta musamman ta kaddamar da bincike a kan tsohuwar kungiyar Yan Tawayen FARC dake kasar Colombia saboda zargin da ake mata na dibar yara kanana sama da 18,000 domin sanya su cikin aikin soji.
Wallafawa ranar:
Minti 1
Talla
A shekarar 2016 kungiyar ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin, kuma daga cikin abinda bangarorin suka amince da shi harda kafa kotun bincike na musamman domin gano irin laifuffukan yakin da aka aikata.
Shugaban kotun na musamman Eduardo Cifuentes yace sanya kananan yara maza da mata cikin yakin ya yiwa al’ummar Colombia matukar illa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu