Isa ga babban shafi

An sake gano gawarwakin mutane a mahakar kwal a Colombia

Hukumar kula da hakar ma'adanai ta kasar Colombia ta sanar da cewa, an gano gawarwakin mutane 15 da suka makale bayan fashewar da ta auku a wata mahakar kwal a arewa maso gabashin kasar makon jiya.

Sansanin masu hako ma'adinai a Colombia
Sansanin masu hako ma'adinai a Colombia © LUIS ROBAYO/AFP
Talla

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an dauki kwanaki 10 tun bayan fashewar wani abu a karkashin kasa a inda aka gano gawar mutun na karshe da safiyar jiya Alhamis.Ranar 30 ga watan Maris ne hadarin ya auku a kantomar Norte de Santander daf da kan iyaka da kasar Venezuela kamar dai yada hukumomin yankin suka tabbatar.

A watan Maris na shekara ta 2021,gwamnati ta soke izinin da aka baiwa wannan kamfani,kafin daga bisani  a watan mayu na shekarar,kamfanin ya sake komawa bakin aikin sa0

Jami'ai sun ce da alama tarin iskar gas ya haddasa fashewa da kuma rushewar kusan kashi 90 na mahakar ma'adinan a garin El Zulia da ke kusa da kan iyaka da Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.