Iran ta zartas da hukuncin kisa kan mutum fiye da 300 a bana - Rahoto
Wata kungiya da ke gwagwarmayar kare hakkin dan adam a Iran ta ce mahukuntan kasar sun zartas da hukuncin kisa kan mutane fiye da 300 a bana kadai, adadin da ba’a ga makamancin sa ba tun 2015.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar wadda ke da Ofishi a kasar Norway, ta ce daga farkon watan Janairu zuwa yau, an kashe mutane 307 ta hanyar rataya karin sama da mutane 75 kan yawan wadanda aka hallaka din a bara.
Kungiyar ta kuma kara da cewa a watan Mayun da ya gabata kadai mahukuntan kasar sun rataye mutane 142, dalilin da ke kara jefa fargaba da razani a zukatan al’ummar kasar, yayin da hakkin dan adam ke fuskantar barzana.
Wani rahoto da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na IHR da ECPM suka fitar a farkon wannan shekara, ya nuna cewa mahukuntan Iran sun kara yawan mutanen da suke zartas wa da hukuncin kisa zuwa kashi 75 cikin 100 a shekarar 2022, matakin da masu kare hakkin na dan adam suka ce ana dauka domin tsorata masu zanga-zangar adawa da gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu