Isa ga babban shafi

An kashe dakarun wanzar da zaman lafiya dubu 4 da 200 a bakin aiki- MDD

Majalisar dinkin duniya ta ce dakarun wanzar da zaman lafiya sama da 4,200 suka rasa rayukansu a sassan duniya cikin shekaru 75 da aka shafe ana tura su yankunan da ake samun tashin hankali domin tabbatar da zaman lafiyar. 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress. © REUTERS / ANDRONIKI CHRISTODOULOU
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ne ya bayyana wannan adadi lokacin da ya ke jinjinawa sojojin da suka sadaukar da rayukansu tun daga shekarar 1948 da aka fara tura su kasashen da ake fama da rikici, tashin hankali ko kuma yake-yake. 

Guterres ya ce lokaci ne na waiwaye domin duba irin nasarorin da aka samu na aikin samar da zaman lafiya, tun daga kasar Liberia zuwa Cambodia da kuma gazawar da aka gani daga Yuguslavia zuwa Rwanda, tare da la’akari da kalubalen da ke tattare da aikin, ciki har da yanayin tashin hankalin da ake fuskanta a duniya a yau da suka hada da labaran karya da sabanin da ake samu wanda ke hana zaman lafiya da kuma dorewar shugabanci ko halastattun gwamnatoci. 

Sakataren ya kuma bayyana cewar duk da ‘yan matsalolin da aka samu, lokaci ne na karrama dakarun samar da zaman lafiya sama da miliyan 2 daga kasashen duniya 125 da suka yi aikin samar da zaman lafiya har sau 71 tun bayan lokacin da kwamitin Sulhu ya tura tawaga ta farko domin sasanta rikicin Isra'ila da Larabawa. 

Guterres ya jinjinawa dakaru 103 da suka rasa rayukansu a shekarar 2022 daga kasashe 39, yayin da ya aje furanni a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya domin karrama wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen irin wannan aikin, inda ya bayyana su a matsayin ginshikin zaman lafiyar fararen hula. 

Sakataren ya kuma bayyana takaicinsa da yadda aikin dakarun samar da zaman lafiyar ke sauyawa daga masu tabbatar da zaman lafiya zuwa na masu fafatawa a fagen daga a wurare masu hadari na duniya. 

Guterres ya bukaci samar da wani yunkuri da yankuna domin magance tashe tashen hankula da yaki da ta’addancin da kasashe 193 dake Majalisar suka amince da su take kuma daukar nauyi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.