MDD ta tsawaita takunkumin haramta cinikin makamai da Sudan ta Kudu
Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya ya kada kuri'ar tsawaita takunkumin hana sai da wa Sudan ta Kudu makamai gami da takunkuman da aka lafta wa wasu daidaikun mutane a kasar.
Wallafawa ranar:
A shekarar 2011 Sudan ta Kudu ta zama kasa mai cin gashin kanta bayan ballaewa daga Sudan, sai dai bayan shekaru biyu kasar ta fada cikin rikicin da ya tagayyara miliyoyin mutane.
Kididdiga ta nuna cewar a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2018, mutane 400,000 aka kiyasta sun mutu yayin da wasu miliyoyi suka rasa matsugunansu, sakamakon yakin basasar da ya barke tsakanin sojoji masu biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma tsagin dakarun da goyon bayan mataimakinsa Riek Machar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu