Isa ga babban shafi

MDD ta zargi jami'an Sudan ta kudu da aikata cin zarafin fararen hula

Wata tawagar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya ta zargi jami’an gwamnatin Sudan ta kudu da hannu a azabtarwa cin zarafi da kuma kisan tarin fararen hular da ya faru a sassan kasar.

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu da mataimakin Riek Machar.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu da mataimakin Riek Machar. AFP - SIMON MAINA
Talla

Bayan samun ‘yanci daga Sudan a shekarar 2011, Sudan ta kudu ta fada yakin basasa bayan rikici da ya faro tsakanin Salva Kiir da Riek Machar wanda ya kai ga mutuwar mutane dubu dari 4 tsakanin shekarar 2013 zuwa 2018 yayinda wasu miliyoyi suka tsere daga kasar zuwa makwabta.

Lamurra sun faro dawowa daidai a jaririyar kasar ne kulla yarjejeniyar kasar ne bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangaren shugaban da mataimakinsa.

Kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya sun ce kaso mai yawa na manyan jami’an gwamnatin Sudan ta kudu da suka aikata tarin laifukan cin zarafin bil’adaman har yanzu na rike da mukamansu a sassan kasar.

Kwarrun sun bayyana sunayen gwamnan jihar Unity Joseph Monytuil da hafson soji Thoi Chany Reat a  matsayin ‘yan gaba gaba da suka aikata laifukan na fyade da cin zarafi baya ga tilastawa tarin mata zama kuyangunsu.

Sai dai tuni gwamnatin ta Juba ta mayar da martani inda ta bayyana bayanan kwararrun majalisar a matsayin masu shirin yi mata shisshigi a lamurranta na cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.