Isa ga babban shafi

Sudan ta Kudu: Gwamnatin rikon kwarya ta kara wa'adin shekaru biyu kafin zabe

Shugabannin Sudan ta Kudu sun sanar da cewa gwamnatin rikon kwaryar kasar za ta ci gaba da mulki, wato karin shekaru biyu bayan wa’adin da aka amince da shi, yayin da abokan huldar kasashen waje suka yi gargadin rashin sahihancin doka a kasar.

Shugaban Sudan ta kudu kenan, Salva Kiir
Shugaban Sudan ta kudu kenan, Salva Kiir REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo
Talla

Martin Elia Lomuro, ministan harkokin majalisar ministocin kasar, ya ce an dauki matakin ne domin tunkarar kalubalen da ke kawo cikas wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, bayan cimma ta a shekarar 2018 na kawo karshen yakin basasan tsawon shekaru biyar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 400,000.

Gwamnatin kasar dai na da nufin kammala wa’adin mika mulki da zabuka a watan Fabrairun shekarar 2023, amma har ya zuwa yanzu ta kasa cimma muhimman tsare-tsaren yarjejeniyar da suka hada da tsara kundin tsarin mulki.

Shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu ya fuskanci tsaiko da dama, inda aka yi tashe-tashen hankula tsakanin dakarun Kiir da na Machar a cikin wannan shekara.

A watan da ya gabata ne Amurka ta fice daga cikin kasashen da ke sa ido kan samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, saboda gazawar kasar wajen cimma muhimman sauye-sauyen da aka cimma.

Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, ta sha sukar shugabannin Sudan ta Kudu kan rawar da suke takawa wajen tada tarzoma, da murkushe ‘yancin siyasa da wawure kudaden jama’a.

Aikin wanzar da zaman lafiya mai dauke da sojoji 17,000 da jami'an 'yan sanda 2,100, na daya daga cikin mafi tsada da Majalisar Dinkin Duniya ke kashewa, inda kasafin kudin shekara ya kai dala biliyan daya.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma zargi gwamnatin kasar da take hakkin jama’a da kuma aikata laifukan yaki kan munanan hare-haren da aka kai yankin kudu maso yammacin kasar a bara.

Sudan ta Kudu, wadda ta kasance guda daga cikin kasashe mafiya talauci a doron kasa duk da dimbin arzikin man fetur, ta sha fama da yaki, bala'o'i, yunwa, rikicin kabilanci da kuma fadace-fadacen siyasa tun bayan samun 'yancin kai a shekara ta 2011.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a watan Maris cewa sama da kashi 70 cikin 100 na al’ummar Sudan ta Kudu miliyan 11 za su fuskanci matsananciyar yunwa a bana saboda bala’o’i da tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.