Isa ga babban shafi

Harin barayin shanu ya kashe mutane 28 a Sudan ta Kudu

Hukumomin Tsaro a Sudan ta Kudu sun ce mutane 28 aka kashe lokacin da barayin shanu suka kai hari a Leer dake Jihar Unity a karshen makon da ya gabata.

Wani makiyayi da shanu a wani yanki na Sudan ta Kudu, 16 ga watan Yuni 2016.
Wani makiyayi da shanu a wani yanki na Sudan ta Kudu, 16 ga watan Yuni 2016. © ALEX MCBRIDE/AFP
Talla

Kwamishinan Yankin Stephen Taker ya bayyana cewar wasu matasa ne suka kai harin daga Yankin Mayendit da Koch dake makotaka da Leer.

Taker yace mutane 10 daga bangaren su sun mutu sakamakon harin, yayin da 18 daga bangaren maharani suka mutu.

Rabaran Stephen Kulang Jiech na mujami’ar Leer yace an kai harin ne yammacin lahadi, yayin da aka ci gaba da fafatawa har zuwa wayewar garin litinin.

Yankin Leer na daya daga cikin Yankunan Sudan ta Kudu da ake gudanar da aikin jinkai sakamakon yakin basasar da aka fara daga shekarar 2013 zuwa 2018 tsakanin magoya bayan shugaban kasa Salva Kiir da na mataimakin sa Riek Machar rikicin da yayi sanadiyar kasha mutane kusan dubu 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.