Isa ga babban shafi

MDD ta yi umarnin gudanar da bincike kan tsanantar aikata fyade a Sudan ta kudu

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu jami’ai na cin zarafin matan da ke sansanin 'yan gudun hijira a Sudan ta Kudu.

Daruruwan mata ne suka gamu da wannan matsala ta cin zarafi a sansanonin 'yan gudun hijira na Sudan ta kudu daga lokacin da aka faro yakin zuwa yanzu.
Daruruwan mata ne suka gamu da wannan matsala ta cin zarafi a sansanonin 'yan gudun hijira na Sudan ta kudu daga lokacin da aka faro yakin zuwa yanzu. Reuters/Andreea Campeanu
Talla

Bukatar binciken daga Sakatare Janar Antonio Guterres ya biyo bayan rahotan hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar wadda ta ce fyade ya zama ruwan dare a sansanin, matakin da ya kai mata basa iya gabatar da korafi akai.

Rahotan ya ce matan basa iya zuwa neman kulawar likita sakamakon fyaden, cikin su har da wadanda gugun maza suka yi musu fyaden a ci gaba da tashin hankalin da ake yi a kasar.

Jami’ar kare hakkin bil adaman, Yasmin Sooka ta ce bincike ya nuna cewar, akwai matan da aka yi wa irin wannan fyade sau 5 a cikin shekaru 9.

Sooka ta ce wasu daga cikin wadannan mata na tambayar su, ko yaushe za’a kawo karshen wannan al’amari ganin yadda aka kwashe dogon lokaci ana yakin, tun daga shekarar 2013.

Jami’ar ta bayyana inda matsalar tafi kamari da suka hada da kauyukan dake Jihar Equatoria da Unity, inda ake ci gaba da gwabza yaki yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.