Isa ga babban shafi

Afrika ta kudu ta kame wasu gungun mutane 80 da suka yiwa Mata 8 fyade

Wani gungun mutane fiye da 80 sun gurfana gaban kotun Afrika ta kudu don amsa tuhuma kan zargin da ake musu na yiwa wasu mata 8 fyade a wani yanayi da hukumar ‘yan sandan kasar ta bayyana da babban abin kunya ga kasar.

Wani yanki a Afrika ta kudu.
Wani yanki a Afrika ta kudu. AFP - IHSAAN HAFFEJEE
Talla

A alhamis din da ta gabata ne gungun ‘yan bindigar suka farwa wani ayarin masu nadar bidiyon waka a gab garin Krugersdorp da ke yammacin birnin Johannesburg tare da yiwa matan 8 fyade mai cike da kankanci.

Hukumar ‘yan sandan Afrika ta kudu ta bayyana matakin da mafi takaici kuma babban abin kunya ga kasar.

A jawabin ministan ‘yan sandan kasar Bheki Cele ya shaidawa manema labarai cewa abin takaici ne samun irin wannan lamari a Afrika ta kudu yana mai cewa da yawa da daga cikin ‘yan matan da suka fuskanci fyaden za su zauna da raunin a zuciyoyinsu har karshen rayuwarsu.

Bayanan da ‘yan sandan kasar suka fitar sun ce ‘yan bindigar sun afkawa ‘yan matan ne lokacin da suke tsaka da shiri don fara daukar bidiyon tare da yiwa 8 daga ciki fyade dukkaninsu kananan yara.

‘Yan sandan dai sun dora alhakin lamarin kan wasu ‘yan cirani da ke aikin hakar ma’adinai a gab da wajen wadanda aka fi sani da Zama Zama kuma tuni aka kame 84 daga cikinsu ko da ya ke an samu musayar wuta gabanin kame su wanda ya kai ga kisan mutum biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.