Isa ga babban shafi
Sudan

An yi wa mata fiye da 10 fyade yayin zanga-zanga a Sudan

‘Yan Sudan sama da dubu daya ne suka gudanar da zanga zanga tare da yin Allah wadai da hare-haren ta’addanci, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mata da ‘yan mata 13 aka yi wa fyade a lokacin wata gaggarumar zanga zangar adawa da mulkin soja

Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Sudan.
Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Sudan. © AFP
Talla

Wannan danyen aikin bai hana masu zanga-zangar fadar “fyade ba zai tsoratar dasu ba”, Jama’ar kuma sunyi ta rera wakoki a babban birnin kasar Khartoum da birnin Omdurman.

Al’ummar yankunan suka ce “zaluncin da aka yi musu , ta hanyar fyade wata dabara ce da aka shirya don raunana musu zuciya, kamar yadda Malaz Kamal mai zanga-zangar ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Hakanan wata daga cikin masu zanga zangar, Nahlan Issa mai shekaru 23 ta ce “suna kokari ne don maido da mutunci da karbar hakkin wadanda aka yi wa fyade kuma za a iya hakanne  kawai ta hanyar tumbuke wannan gwamnati da tayi juyin mulki”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.