Firaministan Sudan ya kori shugabannin 'yan sandan kasar
Fira Ministan Sudan Abdallah Hamdok, ya kori shugabannin rundunar 'yan sandan kasar, bayan da aka kashe fiye da mutane 40 a yunkurin jami’an tsaron na murkushe zanga-zangar da ta biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan jiya.
Wallafawa ranar:
Babban hafsan sojan kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kwace mulki tare da tsare Hamdok a ranar 25 ga watan Oktoba, kafin daga bisani ya sake shi, bayan da kasashen duniya suka yi Allah wadai da matakin.
Bayan zanga-zangar gama gari ta adawa da sojojin na Sudan da ta gudana ne, gami da matsin lambar manyan kasashen duniya, Al-Burhan ya maida da Firaminista Hamdok kan mukaminsa, a karkashin yarjejeniyar da aka kulla a ranar 21 ga watan Nuwamba.
Likitoci sun ce akalla mutane 42 aka kashe yayin da jami’an tsaro ke kokarin murkushe zanga-zangar adawa da juyin mulkin da aka shafe makwnni ana yi, a kasar ta Sudan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu