Isa ga babban shafi
Sudan

Rikicin kabilanci ya hallaka mutane 43 a Sudan

Akalla mutane 43 aka kashe a kwanakin da aka dauka ana dauki-ba-dadi tsakanin makiyaya a yankin Dafur da ke yammacin  Sudan, yayin da kuma aka kona sama da gidaje dubu 1 kurmus.

Yankin Jebel Moon ya yi kaurin suna a rikicin kabilanci tsakanin kabilun larabawa makiyaya da manoma.
Yankin Jebel Moon ya yi kaurin suna a rikicin kabilanci tsakanin kabilun larabawa makiyaya da manoma. - AFP/File
Talla

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne tun a ranar a 17 ga wannan wata na Nuwamba tsakanin Larabawa makiyaya da ke rayuwa a yankin Jebel Moon mai cike da tsaunuka, wanda kuma ke da iyaka da kasar Chadi.

Gwamnan jihar Yammacin Darfur da rikicin ya faru, Khamis Abdallah ya ce rikicin ya faro ne sanadiyyar satar rakuma tsakanin kabilun biyu wanda ya juye zuwa rikicin kabilanci kuma tuni aka aike da dakaru na musamman don tabbatar da zaman lafiyar yankin.

Kwamishinan ayyukan jinkai na jihar yammacin Darfur Omar Abdelkarim da ke tabbatar da rikicin ya ce zuwa yanzu mutane dubu 4 da 300 rikicin ya raba da matsunansu.

Tuni wasu daga cikin mazauna yankin suka tsallaka iyaka domin neman mafaka a Chadi a sanadiyar tarzomar.

Yankin na Jebel Moon da ke da yawan mutane kusan dubu 70 galibinsu manoma da makiyaya da ke kiwon rakuma a lokuta dama suka fuskanci rikicin kabilanci da ke sabbaba asarar dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.