Isa ga babban shafi
Sudan

Al'ummar Sudan sun ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnati

Dubban masu zanga-zanga a Sudan sun sake bazuwa a tituna don kalubalantar yarjejeniyar da kai ga mayar da Firaminista Abdallah Hamdok kan karagar mulki bayan juyin mulkin watan jiya.

Zanga-zangar Sudan ta sauya sabon salo.
Zanga-zangar Sudan ta sauya sabon salo. - AFP
Talla

Dubunnan mutane suka yi dandazo a biranen Khartoum da Omdurman rike da kwalaye masu dauke da rubutun neman kawar da gwamnatin ta Hamdok tare da tabbatar da gwamnatin zallar fararen hula.

Wasu kwalayen na dauke da rubutun ‘‘mulkin fararen hula shi ne zabin al’umma’’ yayinda wasu kwalayen ke dauke da rubutun ‘‘a kawar da ilahirin gwamnatin a maye gurbinta da fararen hula’’.

Kafin juyin mulkin na watan jiya, dai dubunnan ‘yan kasar ne suka rika zanga-zangar nuna goyon baya ga sojoji don su kwace iko da mulki bayan matsin rayuwa da sake durkushewar tattalin arzikin kasar.

Sai dai bayan juyin mulkin na watan jiya bisa jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan al’ummar kasar sun ci gaba da zanga-zanga baya ga matsin lambar kasashen Duniya wajen ganin an mayar da gwamnatin da aka hambarar.

A lahadin da ta gabata ne jagororin juyin mulkin suka mayar da Abdallah Hamdok karagar mulki bisa fatan kawo karshen zanga-zangar da ta kai ga rasa rayukan tarin fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.