Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe jami'an agaji 3 da fararen hula 11 a Sudan ta Kudu

Ofishin kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya OCHA ya sanar da kisan jami’an agaji 3 da fararen hula 11 a Sudan ta kudu cikin watan nan na Janairu, a rikicin da kasar ke ci gaba da fuskanta.

Wani yanki a Sudan ta kudu.
Wani yanki a Sudan ta kudu. © Reuters
Talla

Shugaban ayyukan OCHA a Afrika Peter Van der Auweraert ya bayyna cewa a ranakun farko na sabuwar shekara ne ‘yan bindiga suka kashe jami’an su 3 lokacin da suke kai dauki ga wasu fararen hula da ke rayuwa a wani kauye a yankin da ke da arzikin man fetur.

Auweraert ya bayyana cewa dukkanin jami’an agajin 3 da suka mutu a harin na ranar 2 ga wata ‘yan Sudan ne baya ga fararen hular da harin rutsa da su ciki har da kananan yara wadanda ‘yan bindigar suka kashe cikin rashin imani.

Kakakin gwamnatin yankin Abyei mai arzikin man fetur da harin ya faru, Ajak Deng ya bayyana cewa mutane 14 suka mutu a harin kan garin na county wanda kef ama da hare-haren kungiyoyin mayaka masu rike da makamai.

Yankin na Abyei da ke matsayin kan iyakar kasar ta Sudan ta kudu da kuma makwabciyarta Sudan na fama da rikici ne tun shekarar 2011 lokacin da aka raba kasashen lamarin da ya haddasa asarar dimbin rayuka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.