Isa ga babban shafi

Sudan ta Kudu ta aike da Sojoji 750 DR Congo don taimakawa a yaki da M23

Sudan ta kudu ta sanar da aike dakarun Soji 750 jamhuriyyar demokradiyyar Congo don taimakawa kasar a yakin da ta ke da ayyukan mayakan ‘yan tawayen kungiyar M23 a gabashin kasar.

Dakarun Sojin Sudan ta Kudu.
Dakarun Sojin Sudan ta Kudu. REUTERS/James Akena
Talla

Yayin jawabinsa ga tawagar Sojojin a lokacin da suke shirin tashi zuwa Congo jiya laraba a birnin Juba fadar gwamnatin Sudan ta kudu, shugaba Salva Kiir ya roki dakarun su yi aikin da ya kaisu kasar a tsawon lokacin da za su shafe a can.

A cewar nauyi ne da ya rataya akansu su yi aiki tukuri wajen taimakawa Congo dawo da zaman lafiya musamman a yankin gabashi da kef ama da hare-haren ‘yan tawaye da kuma mamaya a watannin baya-bayan nan.

Dakarun na Sudan ta Kudu kari ne kan dakarun Kenya da Burundi da kuma Uganda da yanzu haka ke taimakawa dakarun sojin Congo wajen yakar barazanar mayakan na M23 da ke ci gaba da zafafa hare-hare a birnin Goma da ke lardin arewacin Kivu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.