Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta tagayyara kusan mutane miliyan guda a Sudan ta kudu

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta OCHA, ta ce ambaliyar ruwa ta shafi mutane kusan miliyan daya a Sudan ta Kudu, dai dai lokacin da matsalar yunwa ke ci gaba da tagayyara al'ummar kasar wadanda ke farfadowa daga yakin basasar shekaru 5.

Wani yanki da ambaliya ta shafe a Sudan ta kudu.
Wani yanki da ambaliya ta shafe a Sudan ta kudu. AFP - PETER LOUIS
Talla

Kididdigar hukumar ta OCHA ta bayyana cewa mutane kimanin dubu dari 9 da 9 ne ambaliyar ruwan ta tagayyara a kasar ta Sudan ta Kudu mai fama da tashe-tashen hankula.

Shekaru 4 kenan a jere da kasar ke fama da ambaliyar ruwa, inda a halin yanzu bala’in ya shafi jihohi tara cikin goma da kasar ke da su.

A jihar Bahr el Ghazal da ke yammacin kasar, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadin rugujewar wata babbar gada, tare da katse isar da kayan agaji ga al'ummar da tuni ke kokawa, kan halin da suke ciki na kunci da bakin talauci baya ga tashin hankali.

Cikin rahoton da ta fitar a watan jiya, hukumar ayyukan jin kan ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane kusan dubu 386 ambaliyar ruwa ta shafa a jihohi bakwai na Sudan ta kudu.

Tun bayan samun 'yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011, Sudan ta Kudu ke cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki da rikicin siyasa, inda su ke fafutukar farfadowa, sakamakon yakin basasar da aka shafe shekaru biyar ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.