Isa ga babban shafi

Rikicin kabilanci ya kashe mutane 173 a Sudan ta kudu- MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda rikicin kabilanci a Sudan ta kudu ya yi sanadin mutuwar mutane 173 tsakanin watan Fabarairu da Mayun shekarar nan, lamarin da ya fi shafar mata da kananan yara.

Wasu 'yan tawaye masu rike da makamai a Sudan ta kudu.
Wasu 'yan tawaye masu rike da makamai a Sudan ta kudu. AFP/File
Talla

Rahoton da majalisar ta fitar yau talata, ta ce Mata da kananan yara sun fuskanci tsananin cin zarafin ciki har da fyade daga gungun masu fyade da suka rika afkawa mata.

Rahotanni sun ce rikici ya barke ne bayan da kungiyoyin da ke rike da makamai magoya bayan shugaba Salva Kiir da masu biyayya ga mataimakinsa Riek Machar ne suka gwabza fada da juna a kananan hukumomin kasar 3 da ke jihar Unity ko kuma al Wahda mai mai arzikin man fetur.   

A cewar bayanai rikicin ya shafi akalla kauyuka 28 wanda ya kai ga kisan fararen hul 173 baya ga sace mata da kananan yara akalla 37.

Rahotan na Majalisar Dinkin Duniya ya ce cikin matan da mayakan bangarorin biyu suka sata har da yara ‘yan shekaru 8 zuwa 9 wadanda suka fuskanci fyade daga mutane da yawa da ya kai ga rasa rayukansu.

Shirin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da rikicin na Sudan da kuma hukumar kare hakkin dan adam sun yi tir da abin da mayakan bangarorin biyu suka aikata.

Rahoton ya bayyana cewa mata da kananan yar ana ci gaba da fuskanta cin zarafi da tsangwama a sassan Sudan ta kudu da kef ama da rikicin kabilanci wanda zuwa yanzu ya tilastawa mutane dubu 44 daga kauyuka 26 tserewa daga matsugunansu a tsakanin lokacin faruwar rikicin.

Rahoton Majalisar ya ce ‘dan tsakanin da aka samu rikicin an samu rahoton fyade da cin zarafi har sai 131 a yankin da aka samu rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.