Isa ga babban shafi

Macky Sall ya ziyarci Sudan ta Kudu don goyon bayan shirin zaman lafiya

Shugaban Senegal Macky Sall ya kai ziyara Sudan ta Kudu, a wani mataki na nuna goyon baya ga shirin samar da zaman lafiya a Kasar.

Shugaban Senegal da Tarayyar Afrika, AU,  Macky Sall.
Shugaban Senegal da Tarayyar Afrika, AU, Macky Sall. © NIPAH DENNIS/AFP
Talla

Tuni dai Shugaba Macky Sall na Senegal ya sauka a filin tashi da saukar jiragen saman sudan ta kudu dake birnin Juba, inda  ya samu tarba mai kyau daga takwararsa na Kasar Sal va Kiir

A zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Kiir,  Sall ya bayyana cewar ya ziyarci Sudan ta Kudu a matsayin Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika AU domin nuna goyon bayansa ga shirin samar da zaman lafiya a Kasar.

Sanarwar da gwamnatin Kiir ta fitar, ta yabawa ziyararsa tare da bayyana ta a matsayin wani yunkuri na samar da dangantaka mai karko tsakanin Kasashen biyu.

Shi ma Edmund Yakani, wani dan gwagwarmaya a Sudan ta Kudu, ya ce ziyarar Shugaban na Senegal zata taimaka wajen gaggauta aiwatar da sauran abubuwan da ke kunshe a shirin zamar da zaman lafiya a Kasar.

Yakani da ya kasance Shugaban wata kungiyar mai zaman kanta dake koyar da sana’oin dogaro da kai ya kuma bukaci Sall da ya matsa kaimi wajen gaggauta aiwatar da sauran batutuwan dake cikin kunshin yarjejeniyar zaman lafiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.