Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Rikicin Sudan ta Kudu na iya zama 'laifukan yaki': Amnesty

Wani rahoton kungiyar Amnesty International ya zargi bangarori masu fada da juna a Sudan ta kudu da sauya salon rikicin da ke tsakaninsu zuwa wani yanayi da ke shafar dimbin fararen hular da ba basu ji ba basu gani ba, wanda za a iya bayyanawa da yunkurin aikata laifukan yaki.

Makaman 'yan tawayen Sudan ta Kudu
Makaman 'yan tawayen Sudan ta Kudu © SUMY SADURNI/AFP
Talla

Amnesty International ta ce fadan na Sudan ta kudu da kuma bangaren adawa da ke samun goyon bayan kungiyoyi masu rike da makamai a dukkannin bangarorin biyu, ya sauya salo a shekarar nan ta yadda ya ke kokarin juyewa zuwa gagarumin yaki da ba a yi tsammani ba.

Rahoton Amnesty ya ce dukkanin bangarorin biyu sun aikata manyan laifukan da suka kama daga kisan fararen hular da basu ji ba basu gani ba, azabtarwa da kuma kone tarin kauyuka, wanda kungiyar ke cewa kai tsaye za a iya bayyana shi a laifukan yaki.

Cikin kunshin bayanan da Amnesty ta fitar ta ce daga watan Yuni zuwa Oktoban da ya gabata, daruruwan fararen hula suka rasa rayukansu a mabanbantan farmakin da bangarorin biyu suka kaddamar kan kauyukan da ke yankin Tambura wanda ta ce siyasa ta yi tasiri wajen raba kan jama’a tare da sanya matasa daukar makamai a hannu.

Daraktan shiyya na Amnesty Deprose Muchena y ace rikicin a Sudan ta kudu yanzu ya juye zuwa wani yanayi da ba a yi tsammani ba, ta yadda mayakan da ke rike da makamai kan farmaki garuruwa su kashe fararen hula tare da kone gawarwakinsu.

Acewar Muchena ba kadai mayakan da ke biyayya ga bangaren adawa ke aikata aika-aikar ba har ma da wadanda ke taimaikawa gwamnatin Juba.

Shekaru biyu bayan samun ‘yanci a 2011 ne Sudan ta kudu ta tsinci kanta a yakin basasa wanda yak ai ga rasa rayukan mutane fiye da dubu 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.