Rikicin Sudan ta Kudu ya zarce na yakin basasar shekaru 5 - MDD
Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya ce rikicin da ke ci gaba da ta’azzara yanzu haka a yankuna da dama na Sudan ta Kudu, shekara daya bayan sanya hannu a yarjejeniyar kawo karshen yakin basasa da aka shafe shekaru 5 ana yi, ya dara na lokacin yakin kansa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahoton da hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce kungiyoyi masu daukar makamai sun zafafa hare hare a kan fararen hula, kuma suna yi ne tare da nuna kabilanci, kuma da goyon bayan gwamnati da dakarun ‘yan adawa.
Shugaban hukumar a Sudan, Yasmin Sooka ta ce rikicin ya zarce wanda aka yi fama da shi daga shekarar 2013 zuwa 2019, tana mai cewa masu hannu a wannan rikici su na yi ne saboda tunanin cewa babu wani mataki da za a dauka a kansu.
An kiyasta cewa yakin basasan da ak gwabza daga shekarar 2013 zuwa 2018 ya lakume rayukan sama da mutane dubu 400, yayin da miliyoyi mutane na kokarin farfadowa daga radadinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu