Isa ga babban shafi
Afrika

Mutane 81 sun mutu a rikicin Sudan ta Kudu

Rundunar Sojin Sudan ta kudu tace akalla mutane 81 suka mutu a jihar Warrap sakamakon barkewar wani kazamin fada tsakanin fararen hular dake dauke da makamai da dakarun gwamnati dake kwance damarar masu dauke da makamai a yankin.

Wasu daga cikinkabilun  Sudan ta kudu dauke da makamai
Wasu daga cikinkabilun Sudan ta kudu dauke da makamai AFP
Talla

Kakakin sojin kasar Lul Ruai Koang yace rikicin ya barke ne a karshen mako lokacin d awasu matasa a Greater Tonj suka fara takalar jami’an tsaro, abinda ya haifar da tashin hankalin.

Koang yace daga cikin mutane 81 da suka mutu, 55 jami’an tsaro ne, yayin da 26 kuma fararen hula ne, bayan wasu 31 da suka samu raunuka.

Jami’in yace an kwashe wadanda suka samu raunuka ta jiragen sama zuwa Juba domin yi musu magani, yayin da hankali ya fara kwanciya a Yankin.

Gwamnatin hadin kan da aka kafa a Sudan ta kudu a watan jiya ta kaddamar da shirin karbe makaman daga hannun jama’a saboda abinda ta kira yadda ake amfani da su wajen rikicin kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.