Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Kungiyar 'yan tawayen Sudan ta Kudu ta nemi gafarar Majalisar Dinkin Duniya

Babbar Kungiyar 'yan tawayen Sudan ta Kudu, wato Sudan People’s Liberation Army In Opposition, ta nemi gafarar Majalisar Dinkin Duniya saboda kama wani jami’in ta da aka yi a watan jiya.

Wasu daga cikin Sojojin 'yan tawayen Sudan ta kudu.
Wasu daga cikin Sojojin 'yan tawayen Sudan ta kudu. AFP
Talla

Wannan ya biyo bayan zargin da jami’an sa ido na Majalisar suka cewar 'yan tawayen sun kama jami’in su tare da wasu fararen hula a kauyen Farajalla da ke Jihar yammacin Bahr El-Ghazal.

Jami’in kungiyar Manjo Janar Martin Abucha ya yi tir da lamarin, yayinda ya nemi gafarar Majalisar Dinkin Duniyar.

Kungiyar 'yan tawayen na daga cikin magoya bayan mataimakin shugaban kasa Rielk Machar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.