Isa ga babban shafi

An samu karuwar aiwatar da hukuncin kisa a duniya - Amnesty International

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa, wato Amnesty International, ta fitar, ya nuna cewa an samu karuwar adadin mutanen da aka yankewa hukuncin kisa a duniya da kashi 53 cikin 100 a shekarar 2022, idan aka kwatanta da shekarar 2021.

Wani jami’in Amnesty Internationa kenan da ya durkusa a kasa, a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke Brussel, ranar 14 ga watan yunin 2021,a matsayin zanga-zangar da ke neman a rufe gidan yarin Guantanamo Bay.
Wani jami’in Amnesty Internationa kenan da ya durkusa a kasa, a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke Brussel, ranar 14 ga watan yunin 2021,a matsayin zanga-zangar da ke neman a rufe gidan yarin Guantanamo Bay. AFP - NILS QUINTELIER
Talla

Rahoton kungiyar ya ce an kashe mutane 883 a kasashe 19 a bara, idan aka kwatanta da 579 da aka samu a shekarar 202, bayan da aka yanke musu hukuncin kisa.

Wadannan alkalumman babu kasar China a ciki, wato bisa bayanan da ke cewa an boye hukuncin kisa a matsayin sirri, inda Amnesty ta yi kiyasin cewa an aiwatar da dubban kisa a kasar.

Kimanin kashi 90 cikin 100 na wadanda aka kashe a duniya banda kasar China, an aiwatar da su ne a kasashe uku kawai wato Iran, Saudiyya da kuma Masar.

A Iran, hukuncin kisa ya karu daga 314 a shekarar 2021 zuwa 576 a shekarar 2022. Yayin da a kasar Saudiyya, hukuncin kisa ya ninka sau uku daga 65 a shekarar 2021 zuwa 196 a shekarar 2022. Masar ta zartar da hukuncin kisa kan mutane 24 a shekarar 2022, kasa da 83 a a 2021.

Akalla kasashe hudu da suka hada da China, Iran, Saudiyya da Singapore sun zartar da hukuncin kisa kan laifukan da suka shafi ta’ammali da muggan kwayoyi wadanda adadinsu ya kai 325 a karshen shekarar 2022.

Rahoton ya ci gaba da cewa, har kasashe hamsin da biyar har yanzu suna aiwatar da hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifukan da suka danganci hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.