Isa ga babban shafi

Mutumin da ya kashe makwabtansa 5 a Amurka ya shiga komar 'Yan sanda

Jami’an tsaro a Tezax na kasar Amurka suka ce sunyi nasarar cafke mutumin nan da ake zargi da kashe wasu makwabtansa biyar saboda sun bukaci ya daina harbin bindiga da yake yi a farfajiyar gidansa, bayan kwashe kwanaki ana farautarsa.

Jami'an 'yan sandan kasar Amurka.
Jami'an 'yan sandan kasar Amurka. Carlo Allegri / Reuters
Talla

Francisco Oropesa dai ya shiga wasan buya da jami’an tsaro tun bayan kisan da ya yi ranar Juma’a a karamin garin Cleveland da ke kudu maso gabashin Texas.

Jami’an tsaro suka ce an kama mutumin ne a karkashin wasu kayan wanki acikin wani kabad.

Ana zargin dan kasar Mexico mai shekaru 38 da kai wa makwabtansa hari bayan da suka nemi ya daina harbin bindigar sa mai sarrafa kanta ta AR-15 saboda hayaniya ta sa jaririnsu ya tashi.

Hukumomin kasar sun baza daruruwan jami’an tsaro domin nemo wanda ake zargin tare da bayar da tukuicin dala 80,000 ga duk wanda ya bada bayanin da ya kai ga kama shi.

Jami’in hukumar FBI na musamman Jimmy Paul ya shaidawa manema labarai jiya talata da daddare cewa kiraye-kirayen da aka yi wa layukan ofishin a karshe ya jagoranci jami’an tsaro zuwa Oropesa, wanda aka kama a arewacin Houston da misalin karfe 6:45 na yamma agogon kasar (2345 GMT).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.