Isa ga babban shafi

Antonio Guterres na ziyara a Kenya domin samo mafita game da rikicin Sudan

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya isa kasar Kenya domin tattaunawa game da batun yakin Sudan, inda zai tattauna game da sha’anin tsaron kasar tare da shugaba William Ruto.

Antonio Guterres lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraqi.
Antonio Guterres lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraqi. © Hadi Mizban / AP
Talla

Babba manufar ziyarar ita ce batun tsaro da jin kai a Sudan da kuma yin shawarwari da dukkan shugabannin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke taro a Nairobi cikin wannan mako, in ji ministan harkokin wajen Kenya Alfred Mutua.

A farkon wannan makon, shugaba Ruto ya ce Nairobi za ta hada kai da taimakon jin kai ga Sudan, inda ake sa ran sama da mutane 800,000 za su fice daga kasar saboda rikicin da ake fama da shi.

Yaki ya barke a birnin Khartoum ranar 15 ga watan Afrilu bayan da dakarun da ke biyayya ga Janar Mohamed Hamdan Daglo suka yi artabu da sojojin kasar Sudan da ke yin mubaya'a ga shugaban gwamnatin mulkin soji, Janar Abdel Fattah al-Burhan.

A ranar Talatar da ta gabata, manyan hafsoshin sojojin biyu da ke fada da juna sun amince da tsagaita bude wuta na kwanaki bakwai bayan da wakilan yankin suka yi tir da cin zarafin da ake yiwa fararen hula.

Sudan ta Kudu ta ce duk da kokarin da ake yi a diflomasiyyance, hakan ya gaza kawo karshen yakin da ya addabi kasar da ta kasance ta uku mafi girma a Afirka sama da makonni biyu yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.