Isa ga babban shafi

Sudan ta sauya gwamnan Blue Nile bayan rikicin kabilanci ya kashe mutane 200

Gwamnatin Sudan ta sanar da nadin sabon kwamandan soji a matsayin gwamnan jihar Blue Nile mai fama da rikici, inda a baya bayan nan rikicin kabilanci da ya barke ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 200.

Shugaban gwamnatin Sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan.
Shugaban gwamnatin Sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan. © Monicah Mwangi / Reuters
Talla

Matakin ya zo kwana guda bayan da shaidun gani da ido suka bayar da rahoton cewa dubban mutane sun yi zanga-zanga a gaban hedkwatar sojojin da ke Damazin babban birnin jihar ta Blue Nile, suna zargin gwamnati da gaza kare su, tare da dakatar da jami’ar yankin.

Blue Nile da ke kan iyaka da Sudan ta Kudu da Habasha, na fama da matsalar yaduwar makamai tare da fafutukar sake gina gine-ginen da aka rusa bayan yakin basasa na shekaru da dama.

Bangarorin kabilun da ke rikici da juna a yankin dai na samun makamai ne daga kasashen Habasha da Sudan ta Kudu wadanda ke fama da yakin tsawon shekaru, dalilin daya sa a duk lokacin da rikicin kabilanci ya barke ake samun asarar dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.