Isa ga babban shafi

Salva Kiir na kokarin sasanta bangarori dake rikici a makwabciyarsa Sudan

Gwamnatin Sudan ta kudu ta ce bangarorin dake rikici da juna a Sudan sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 7, biyo bayan korafin da tawagar kungiyar yankin gabashin Afrika ta yi a kan su, na kin mutunta matakin tsawaita tsagaita wuta sau biyu.

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir. 02/05/23
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir. 02/05/23 AP - Brian Inganga
Talla

Cikin sanarwar da Ma’aikatar harkokin wajen sudan ta kudu ta fitar, ta ce  Shugaban rundunar sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo da a yanzu suka koma abokan gaba, sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 7, daga ranar 4 ga watan mayun nan da muke ciki zuwa 11 ga wata. 

Rashin mutunta yarjejeniya

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tun bayan barkewar rikicin kasar a ranar 15 ga watan afrilun da ya gabata, saidai daga bisani bangarorin na kin mutunta matakin, lamarin da ya haifaar da caccaka daga Kasashen duniya.  

Biyo bayan gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na cewa Sudan na dab da rugujewa, aka kara tsananta yunkurin diflomasiya wajen ganin an kawo karshen rikicin da aka shafe sama da mako 2 ana gwabzawa a kasar da ta kasance ta 3 mafi girma a yankin Afrika. 

Majalisar Dinkin Duniya tace ya zuwa yanzu daruruwan mutane suka rasa rayukansu a rikicin, yayin da wasu dubbai suka jikkata, sannan sama da mutane dubu 430 ne suka tsere daga gidajensu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.