Yakin Sudan ya raba sama da mutane dubu 400 da gidajensu
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari 3 da 30 ne rikicin Sudan ya sanya su barin gidajen su, inda kuma wasu sama da dubu dari suka bar kasar.
Wallafawa ranar:
Hukumar Kula da ‘Yan Cirani na Majalisar ta yi kiyasin cewa, kimanin mutane dubu dari 3 da 34 ne ke gudun hijira a cikin kasar tun bayan barkewar rikicin a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata.
Adadin mutanen da suka yi gudun hijira a cikin makwanni biyu da fara rikicin, ya zarce adadin gaba daya wadanda suka yi gudun hijira a rikicin kasar na shekarar 2022.
Har wayau, Kakakin Hukumar Bada Agaji na Majalisar Jens Laerke ya ce kashi 14 ne kadai aka samu na yawan gudunmuwar da ake bukata a gidauniyar bada agaji ta kasar da aka samar a wannan shekarar, inda a yanzu akwai gibin kusan dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari biyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu