AU ta yi kira da a taimaka wa fararen hula da ke tserewa rikicin Sudan
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira ga makwabtan Sudan da kasashen duniya da su taimaka wa mutanen da ke gujewa mummunan fadan da ake gwabzawa a can tare da sabunta kiran tsagaita bude wuta.
Wallafawa ranar:
Cikin wata sanarwa ofishin Shugaban hukumar ta AU Moussa Faki Mahamat ya ce suna ci gaba da sanya ido tare da nuna matukar damuwa game da halin da fararen hula ke ciki a rikicin kasar Sudan.
Faki ya kuma yi kira ga sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF da su gaggauta amincewa da tsagaita bude wuta na dindindin domin saukaka kai agajin jin kai ga mutanen Sudan da ke cikin tsananin bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu