Isa ga babban shafi

An cigaba da gwabza fada a Sudan bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

Jiragen yakin sojojin Sudan sun yi ta ruwan bama-bamai kan dakarun kai daukin gaggawa na RSF a Khartoum, yayin da kuma a jiya Alhamis sabon fada ya barke a yankin Darfur.

Wani yanki na Khartoum babban birnin kasar Sudan.
Wani yanki na Khartoum babban birnin kasar Sudan. AFP - HANDOUT
Talla

Lamurran sun auku ne bayan da bangarorin masu rikici da juna, suka amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da karin kwanaki 3, bayan karewar ta farko.

Yarjejeniyar farko itama ta tsawon kwanaki uku da aka sha karyawa ta kare ne a daren jiya Alhamis, sai dai gabanin karewar wa’adin ta, shugaban mulkin sojin Sudan Janar Abdul Fattah al Burhan, da kuma babban kwamandan dakarun RSF Muhammed Hamdan Daglo, suka amince kara wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta, biyo bayan matsin lamba daga Saudiya da Amurka.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kungiyar Tarayyar Afirka, Majalisar Dinkin Duniya, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Birtaniya da Amurka sun yaba da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi, da kuma yadda bangarorin sojin masu rikici da juna suka amince da zurfafa tattaunawar sulhu.

Ya zuwa yanzu akalla mutane 512 suka mutu, wasu 4,193 kuma suka jikkata a fadan na Sudan, sai dai jami’an lafiya sun ce yawan mamatann ka iya zarta wanda aka bayyana da  adadi mai yawa.

Tuni dai bangaren kiwon lafiya ya ji jiki matuka a kasar, domin kuwa ruwan bama-baman da ya shafi asibitoci ya sa sama da kashi biyu bisa uku ba sa aiki a birnin Khartoum kamar yadda kungiyar likitoci ta tabbatar.

Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce kazamin fadan na Sudan na iya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa, domin kuwa a halin yanzu ma alkalumma sun nuna cewar akalla kashi 1 bisa 3 na yawan ‘yan kasar miliyan 15 ke bukatar agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.